
Wani matashi ɗan shekara 18, mai suna Adamu Musa, mazaunin Unguwar Magina, a cikin garin Buji da ke Ƙaramar Hukumar Buji a jihar Jigawa, ya rasa ransa a wani tafki a lokacin da ya ke ƙoƙarin ceto saniyarsa da ta zame ta faɗa a lokacin da ya ke kiwo a yankin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar tsaron farar hula, NSCDC, reshen jihar Jigawa, CSC Adamu Shehu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Lahadi.
Ya ce lamarin ya faru ne a jiya Asabar, da misalin karfe 02:00 na rana, lokacin da matashin ya kaɗa shanunsa guda biyu zuwa gona, ya kuma bar su su yi kiwo a kusa.
Ya ƙara da cewa ɗaya daga cikin shanun sai ta zame ta faɗa cikin ruwan da ke kusa da gonar da su ke kiwon.
PRO ɗin ya ƙara da cewa, a lokacin da saniyar ta faɗa, sai Adamu ya yi maza ga bita cikin ruwan domin ya ceto ta, amma sai ya nutse a ciki.
Shehu ya ce duk ƙoƙarin da mutanen yankin da jami’an NSCDC suka yi na ceto shi, ba a sami gawarsa ba sai karfe 01:00 na safiyar Lahadi.
“An kai gawar asibiti, inda a ka bincika ta sosai aka tabbatar da mutuwarsa, sannan aka mika wa iyayensa domin su yi musu jana’iza yadda ya kamata, inda ita kuma saniyar a ka ce to ta da ran ta,” in ji Shehu.