Home Siyasa Shekarar 2022 shekara ce ta sulhu da zaman lafiya – Ganduje

Shekarar 2022 shekara ce ta sulhu da zaman lafiya – Ganduje

0
Shekarar 2022 shekara ce ta sulhu da zaman lafiya – Ganduje

 

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce ya kamata sabuwar shekara ta 2022 ta kawo sabon zaman lafiya da sulhu a tsakanin masu ruwa da tsaki a jam’iyyun siyasa a jihar da ma ƙasa baki ɗaya.

Gwamnan ya ce ya kamata a ce watanni masu zuwa su zama na siyasar cikin gida, inda za a samu ci gaba a jam’iyyun siyasar jihar, inda ya ƙara da cewa yin hakan zai samar da wakilai masu nagarta a matakai daban-daban wadanda su ke da ƙwarewar da za su ci gaba da gina Kano kan tsare-tsare da manufofin da shugabannin da su ka shuɗe su ka assasa.

A saƙon sabuwar shekara ga al’ummar jihar, wanda Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar, gwamnan ya ce da ga dukkan alamu abubuwan da su ka faru a Kano na iya kawo wani sabon salo a tarihin siyasar jihar.

Ya ce al’ummar Kano da ke da kishin cigaban jihar sun nuna buƙatar ganin manyan ƴan siyasar jihar sun yi sulhu da juna, domin ganin an samar da zaman lafiya da ci gaba mai inganci a fagen siyasa da al’amuran cigaban al’umma.

Sanarwar ta nuna matuƙar damuwa kan yadda ake ta fama da taɓarɓarewar tsaro a faɗin ƙasar, baya ga fatara da a ke fama da ita sakamakon taɓarɓarewar tattalin arziki a ƙasa.

Sai dai ya bayyana fatansa na cewa duk da ƙalubalen da a ke fuskanta, gwamnatin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari na ci gaba da ƙoƙarin ganin an aiwatar da manufofinta da shirye-shiryen yadda za a ragewa al’umma radadin talauci.

Gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa gwamnatin sa, wacce kasafin kuɗin 2022 ya maida hankali wajen kammala aiyuka, da ƙudurin aniyar kyautata wa al’umma ta hanyar kawo sauyi a yankunan karkara da kuma shirye-shiryen karfafa tattalin arzikin Jihar Kano.

Yayin da yake taya al’ummar kasar murnar shigows sabuwar shekara, Ganduje ya kuma yi kira da a hada kai da yi wa Najeriya addu’a musamman malaman addini su rika wa’azi akan zaman lafiya, hakuri da juna duk da kalubalen da ake fuskanta.