Home Siyasa Shekarau ya samu tikitin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a NNPP

Shekarau ya samu tikitin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a NNPP

0
Shekarau ya samu tikitin takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a NNPP

 

 

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya yi nasarar lashe tikitin takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a karkashin jam’iyyar NNPP.

A zaɓen da aka gudanar a Ƙaramar Hukumar Gezawa, ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da ke ƙarƙashin majalisar dattawa, Malam Ibrahim Shekarau ya samu ƙuri’u 516.

Shekarau, wanda shi ne Sanata mai wakiltar shiyyar a majalisar dokokin Najeriya, a jawabinsa, ya gode wa Allah maɗaukakin sarki da ya sanya aka samu nasarar kammala zaɓen cikin nasara.

Shekarau ya sauya sheƙa ne da ga jam’iyar APC zuwa NNPP, inda daga shigar da ya samu fom ɗin takarar kujerarsa ta Sanatan Kano ta Tsakiya a sabuwar jam’iyar da ya koma.