Home Siyasa Shekarau ya sansanta da Ganduje

Shekarau ya sansanta da Ganduje

0
Shekarau ya sansanta da Ganduje

 

Tsohon Gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau ya sansanta da Gwamna mai ci, Dakta Abdullahi Ganduje, kamar yadda Daily Nigerian Hausa ta gano.

Idan za a iya tuna wa, APC ta dare gida biyu a Kano tun bayan zaɓen shugabannin jam’iya na jiha, inda Shekarau ya jagoranci ɓangare ɗaya, ya kuma tsayar da Amadu Haruna Zago a matsayin shugaban jami’ya, shi kuma Abdullahi Abbas, a matsayin shugaban jam’iyar na tsagin Ganduje.

Haka a ka ci gaba da tafiya har ta kai ga ɓangarorin sun dangana ga kotun ƙoli, inda yanzu a ke jira ta yanke hukunci.

Sai dai kuma a bisa bayanan da wannan jarida ta samu, tuni dai Shekarau ya zagaye ya sasanta da Ganduje, kuma har yanki fom ɗin sake tsaya wa takarar Sanata, bayan an daddale da shi cewa za a dawo masa da takarar sa

Wannan jaridar ta jiyo cewa Shekarau da Ganduje sun raba dare a ranar Litinin, har zuwa awannin farko na Talata su na wata ganawar sirri domin sulhunta wa, inda daga ƙarshe dai a ka yarda cewa Shekarau zai koma kujerarsa ta Sanata.

Haka zalika an jiyo cewa sansanta war ta biyo bayan kiran da Shugaban APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu ya yi na cewa a sansata da duk wani tsohon Gwamna da ke Majalisar Dattawa a kuma sake bashi takara a 2023.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa a yau Juma’a ne kuma Shekarau da Ganduje za su rankaya zuwa Abuja domin gana wa da Shugaban na APC na Ƙasa domin sake ƙarfafa sulhun da a ka yi tsakanin shugabannin biyu.

Tuni dai wannan lamari ya harziƙa magoya bayan G-7, har ya haifar da cecekuce, musamman tsakanin ɓangaren Sanatan Kano ta Arewa, Barau Jibrin da kuma na Shekarau ɗin.

Sai dai kuma Kakakin Shekarau, Sule Ya’u Sule, ya musanta batun cewa tsohon gwamnan ya bar ɓangaren G-7.

Ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa har yanzu Shekarau shi ne shugaban G-7, inda ya ƙara da cewa har yanzu ɓangaren na tafiya tare kuma duk wani mataki a na ɗauka ne tare.

Sule ya ƙara da cewa fom ɗin da Shekarau ya siya ba wai yana nufin ya bar ɓangaren bane, inda ya ce sauran masu ra’ayin takara ma a G-7 duk sun sayi fom domin lokacin da a ka sanya da farko za a rufe sayar da fom ɗin yau ne Juma’a, kafin daga bisani jam’iyar ta ƙara kwanakin rufe sayar da fom ɗin.