
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanatan Kano ta tsakiya Ibrahim Shekarau, ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar NNPP daga APC.
Tsohon gwamnan shi ne ya bayyana hakan yayin wani gangamin taro da ya gudana a gidansa na Kano a yau Laraba.
Yayin taron dai, Shekarau ya bayyana da bakinsa cewa ya fice daga Jam’iyyar APC, inda ya koma NNPP mai alamar kayan marmari.
Jim kaɗan bayan Shekarau ya sanar da sauya shekar sa zuwa NNPP, Jagoran jam’iyar na ƙasa, Rabi’u Musa Kwankwaso, sai ya miƙa wa Shekarau ɗin fom ɗin takarar Sanata Kano ta Tsakiya.
An dai Jima ana jiran ficewar Shekarau da ga Jam’iyyar APC duk kuwa da kokarin sulhu da aka so yi tsakanin ɓangaren gwamnatin Kano da tsohon gwamnan amma bai yiwu ba.