
Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu, ya gayyaci tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau, zuwa wata gana wa a ranar Laraba a Abuja, kamar yadda majiya mai tushe da ke da masaniya a kan lamarin ta shaidawa DAILY NIGERIAN.
Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC ya gayyaci Malam Shekarau, wanda shine dan takarar kujerar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar NNPP, zuwa ganawar domin ya jawo shi cikin jam’iyyar.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa Malam Shekarau ya riga ya cimma matsaya da ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, kan ya koma jam’iyyar da kuma jagorantar yakin neman zaɓensa a yankin Arewa maso Yamma.
Wani jigo a jam’iyyar PDP a Kano ya shaida wa wannan jarida cewa jam’iyyar ta fara tattaunawa yadda za ta gyara tsarinta don yi wa Shekarau waje a cikin ta.
A cewarsa, mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na shiyyar, Bello Hayatu Gwarzo, ya sanar da jiga-jigan jam’iyyar a jihar game da zuwan Malam Shekarau da shirin karbarsa da mukarrabansa.
Wannan jarida ta samu tabbacin cewa abokin takarar Tinubu, Kashim Shettima, ya gana da Malam Shekarau a ranar 8 ga watan Agusta, amma majiyoyin sun ce “ba a cimma yarjejeniya ba”.
Duk da cewa masu lura da al’amura sun ce tsohon gwamnan ya riga ya yanke shawarar komawa jam’iyyar PDP, amma shi – a bisa ka’ida – ya gayyaci majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa, majalisar shawara ta Shura, domin ta ba shi shawara.
Ana sa ran majalisar za ta gabatar da rahoto a yau kuma za a sanar da yanke shawara a cikin makon nan.