
Daga Adam Ahmad Muhammad
A lokacin da Joshua Dariye ya zama gwamnan Filato ya zo da kin Hausawa a ransa kuma yana ganin dama ta samu da zai koresu daga fadin jihar, yayi iya abinda yayi, da Jonah Jang ya zo sai aka yi sa’a ra’ayinsa daya da Dariye don a lokacin sai shawo kan rikicin ya gagara saboda su suke so a yi. Amma da Allah ya kawo Lalong da ba ya sha’awar rikicin yanzu ga Filato nan ta zauna lafiya ba wata tashin tashina, an ce har Allah wadai yake yi da dokar kiwo da Benue da Taraba suka saka ya ce dokar za ta kawo tashin hankali ne.
Darius da Ortom su ma ‘yan’uwan Dariye da Jang ne, mutane ne masu kaunar kabilarsu kawai kuma sun tsani Fulani ba sa kaunarsu, shi ya sa suke ganin dama ta samu da za su karar da Fulani daga jihohinsu.
Tun farko Darius ya fara cewa lallai Fulani sai su rage yawan shanunsu wai, da haka ba ta samu ba shine aka hau fulanin Mambila da kisan kare dangi, kisan da wani hafsan soja ya ce kisa ne na kare dangi saboda kowa da komai kashewa ake yi.
Inda za ku gane da sa hannun gwamna aka yi shine, an kashe mutane sama da 800 amma har yanzu bai fito ya jajanta ko ya nemi a dauki kowane irin mataki akan makasan ba, an ce ma har mukami ya ba wanda ake zargin shine ya jagoranci kisan, kar mu manta fa su fulanin Mambila ba yawon kiwo suke yi ba balle a ce sun yiwa manoma barna, to meye laifinsu? Kawai gwamna ba ya kaunarsu don haka yake son sai an koresu daga yankin.
Shi kuwa Ortom ko ba a fadi ba kun san ajandarsu daya da Darius, ya saka dokar kiwo kuma ya ba wasu yan daba makamai ya ce duk inda suka ga Fulani a jahar su kashe, haka kuwa suke ta yi, lokacin da aka kashe yan kabilarsa sama da goma ba irin ihun da bai yi ba, sai da kasar nan aka daina komai in banda maganar Benue killings, amma duk fulanin da ake kashewa ba ruwansa, ba zai jajanta ba, ba zai dauki mataki ba, ko maganar ba zai yi ba, saboda kawai haka yake so kuma a bisa umarninsa ake aikatawa.
To irin wannan rigimar da gwamna yake goyon baya tana da wahalar lamari, saboda ko ba komai gwamna shine babban jami’in tsaro a jiharsa, don haka duk jami’an tsaron da za’a kawo dole da shi za’a yi aiko, don haka ko dai su bi abinda yake so kokuma a yi ta samun sabanin da a karshe jami’in tsaron ne zai kwana a ciki saboda gwamnan ne yake da goyon bayan kundin tsarin mulki.
Maganin irin wannan rikici ma fi sauki shine a canja gwamnan da wani da ba mai son fitina ba ne, 2019 tana kusa, duk da cewa gwamnan Benue zai yi wahalar canjawa saboda jam’iyyarsa ta na da karfin da da wahala jam’iyyar adawa ta kayar da ita a jihar, amma shi Darius za’a iya kayar da shi tunda APC ta na da karfi a jihar, to ya zama wajibi mutanen Taraba su hadu su kau da wannan annoba da take son yin kaca-kaca da jihar saboda kawai gwamnan ba ya son wata kabila.
Shi kuwa na Benue gwamnatin tarayya da majalisar kasa ta yi kokarin nuna masa kuskurensa don ya gyara, idan ya ki a tafi a haka dole lokacin sauka zai zo kuma dole ya sauka, Fulani kuwa yayi kadan ya ce zai iya karar da su a cikin shekaru takwas, da hakan mai yiwuwa ne da Dariye da Jang sun karar da Hausawan Jos a cikin shekaru 16, amma haka suka yi suka gama har yanzu akwai hausawa a can, ga shi har Allah ya kawo Luling da shi kuma son zaman lafiya ne a ransa, su kuwa burinsu bai cika ba kuma tarihi ya rubuta duk abinda suka yi kuma ana kallonsu da shi.
Sannan kowacce jiha ta rika lura da duk wani dan takarar gwamna da ake ganin mai mugun kabilanci ne a daina ba shi dama, saboda irinsu ba alheri ba ne ga kasa!