
Idan a na maganar ɗan ƙwallon ƙafar da ya fi kowa kuɗi a wasan, ba wanda zai zo ma ka a rai sai Lionel Messi ko Cristiano Ronaldo.
To ai kuwa abin ba haka bane, domin kuwa wanda ya fi kowanne ɗan ƙwallon ƙafa kuɗi ba sananne ba ne, inda yanzu haka ma ya koma taka leda a ƙasar Thailand.
Shi dai wannan ɗan wasa da ya fi kowanne ɗan ƙwallon ƙafa arziƙi a duniya shine Faiq Bolkiah.
An haifi Bolkiah a ranar 9 ga watan Mayu, 1998 a Los Angeles da ke California a Amurka.
Shi dai wannan matashin ɗan ƙwallo ɗan sarauta ne sabo da mahaifinsa, Jefri Bolkiah, ɗan gidan Sarkin Brunei ne kuma hamshaƙin mai kuɗi ne.
A taƙaice, Bolkiah ya fara rayuwar ƙwallon ƙafa ne AFC Newbury, inda da ga bisani ya yi gajeren zamani a Southampton da ke Britaniya.
Da ga nan ne sai ya samu ci gaba inda ya shiga ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Leceister City da Chelsea.
Abinda ya sa Bolkiah ya fi kowanne ɗan ƙwallon ƙafa arziƙi shine, ya gaji dukiyar mahaifinsa ne, inda a halin yanzu, ɗan wasan mai shekara 23, ke da kuɗi wuri na gugar wuri har fam biliyan 13 (£13, 000, 000, 000).
A yanzu haka, ƙaunar Bolkiah da ƙwallon ƙafa, wanda ɗan ƙanin Sultan na Brunei ne, ya sauya sheƙa zuwa Thailand minnows Chonburi FC.