Home Labarai A shirye mu ke mu ci gaba da yajin aiki har sai an biya mana buƙatunmu — ASUU

A shirye mu ke mu ci gaba da yajin aiki har sai an biya mana buƙatunmu — ASUU

0
A shirye mu ke mu ci gaba da yajin aiki har sai an biya mana buƙatunmu — ASUU

 

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i, ASUU, ta ce mambobinta za su ci gaba da jajircewa wajen ganin cewa jami’o’in gwamnati sun samu abinda su ke bukata daga Gwamnatin Tarayya don samun ci gaba da yin takara da jami’o’in ƙasashen duniya.

Farfesa Ayo Akinwole, shugaban ƙungiyar ASUU na jami’ar Ibadan ne ya bayyana hakan a jiya Litinin a Ibadan.

Akinwole ya ce malaman jami’o’in gwamnati a Najeriya na amfani da jininsu wajen tafiyar da jami’o’in gwamnati da kuma ci gaba da gudanar da ayyukansu.

“Malamai sun rike jami’o’in gwamnatin Najeriya da jininsu, amma shin ya dace ‘yan Najeriya su ce su je su mutu a bakin aiki? Ina sanar da ku cewa suna mu na bin alawus ɗin mu na sama da shekaru takwas.

“Shin ASUU ne kawai ke yajin aiki? Wasu sassa (cibiyoyin bincike) na kasar nan sun kwashe watanni 13 suna yajin aiki kuma gwamnati na biyansu albashi.

Shin laifi ne zama malami a jami’o’in Najeriya? Me ya kai ga yajin aikin? Rashin mayar da hankali ne na gwamnati ya sa aka fara yajin aikin,” inji shi.

A cewarsa, kungiyar ba za ta sarayar da walwalar mambobinta ba, inda ya nanata cewa zai bijirewa duk wani yunƙuri na mayar da masu ilimi zuwa bayi.