
Kusa a cikin jam’iyyar APC ta jihar Kaduna, Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya fice daga jam’iyyar, ya kuma bayyana Shugaba Buhari a zaman wanda saam bai cancanci shugabancin Najeriya ba. Sanata Babaa-Ahmed yana bayyana hakan ne a lokacin da yake ayyana komawarsa jam’iyyar PDP mai hamayya.
Tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya daga 2003 zuwa 2007, kuma tsohon sanata a rusasshiyar jam’iyyar CPC, wanda ya kayar da tsohon Gwamnan jihar Kaduna kuma Shugaban jam’iyyar PDP na riko na yanzu Ahmed Mohammed Makarfi.
Sanata Yusuf Datti Baba-Ahmed ya zargi jam’iyyar APC da shararawa ‘yan Najeriya karya, ya kuma duk batun da ake yi da sunan yaki da cin hanci da rashawa duk burgace ba gaskiya ben, yace ba komai bane sai biri boko da ake yiwa ‘yan najeriya.
Shin me zaku ce kan wannan zargin?