
A yau Shugaba Muhammadu Buhari ya hadu da tsaffin Shugabannin Najeriya, Olushen Obasanjo da Abdulsalami Abubakar a wajen babban zauren kungiyar kasashen AFurka, a taron da ake gudanarwa na kungiyar karo na 30 a birnin Adis Ababa na kasar Habasha.
Wannan dai shi ne karon farko da aka hadu tsakanin Obasanjo da Buhari tun bayan da Obasanjon ya aikewa da Buhari wata wasikar da yake gargadinsa da sake tsayawa zabe a 2019.