
shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya isa jihar Zamfara, inda zai halarci wani taron tattaunawa da al’umma domin tattauna matsalolin tsaron da suke damun jihar kamar yadda yayi a Taraba da Borno da Yobe da Binuwa.
Kamfann dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewar, Shugaban wanda yake tare da rakiyar mukarraban Gwamnatinsa ya isa Gusau babban birnin jihar da misalin karfe 10:40 na safiya, bayan da ya taso daga filin sauka da tashin jiragen sama na Umaru Musa YarAdua dake Katsina.
Gwamnonin jihohin Sakkwato AMinu Waziri Tambuwal da na Kebbi Atiku Abubakar Bagudu da Sarakunan Gargajiya da Malaman addini da manyan mukarraban Gwamnatin tarayya na daga cikin wadan da suka marabci Shugaban kasa a jihar.
Shugaba Buhari ya karbi faretin bangirma daga jami’an sojan saman Najeriya.

An tsara cewar Shugaban zai yiwa Sarakunan gargajiyar jihar wani jawabi da kuma masu ruwa da tsaki a jihar. Sannan kuma, zai jajantawa iyalan wadan da aka kashe musu ‘yan uwansu a kashe kashe da aka yi kwanakin baya a jihar.
Jihar Zamfara dai ta sha fama da hare haren ‘yan sari ka noke da kuma ‘yan bindiga dadi, daruruwa mutane aka kashe wadan da basu san hawa ba balle sauka, sannan kuma an barnata dukiyoyi na biliyoyin nairori.
Harin baya bayan nan da aka kai jihar shi ne wanda aka kai a kauyen Birani dake yankin karamar hukumar mulkin Zurmi inda aka kashe akalla mutane 50 har lahira.
Daya daga cikin fitattun ‘yan ta’addar jihar, wanda ake kira da Tsoho Buhari ko kuma sunan da yafi shahara da shi wato Buharin Daji, an kashe shi a ‘yan kwanakin da suka gabata a jihar.
NAN