
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya baro birnin Landan na kasar Burtaniya zuwa, Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, bayan da ya kammala halartar taron kasashen da ingila ta yiwa mulkin mallaka.
Shugaban ya shafe kwanaki a Landan yana ganawa da mutane da kungiyoyi daban daban a yayin da yaje wannan muhimmintaro, inda a can ne Shugaban yayi jawabin da ya harzuka matasa da yawa a Najeriya, inda ya kirasu da masu zaman banza ko zaman kashe wando.
An ruwaito cewar, Shugaba Buhari yana bayyana matasan Najeriya da cewar kaso 60 ba su da ilimi, kuma cima zaune ne, masu jiran samun komai kyauta. Wadannan kalaman ba su yiwa matasa da yawa dadi ba, inda aka yi ta caccakar Shugaban a kafafen sada zumunta na intanet.