Home Kanun Labarai Shugaba Buhari ya bar Najeriya zuwa Faransa

Shugaba Buhari ya bar Najeriya zuwa Faransa

0
Shugaba Buhari ya bar Najeriya zuwa Faransa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar babban birnin tarayya Abuja zuwa birnin Faris na kasar Faransa da safiyar Juma’ar nan domin halartar wani taro kan Zaman lafiya.

Kasar Faransa ce ta shirya taron kuma ta gayyaci Shugaba Buhari domin tattaunawa kan batun Zaman lafiya a duniya. A yayin taron ana sa Rab Shigaba Buhari zai gana da Shugaban kasar ta Faransa Emmanuel Macron.

Haka kuma Shugaba Buhari zai yi wata ganawa ta musamman da Sakatare janar na majalisar dinkin duniya a birnin na Faris. Taron dai za a shafe kimanin kwanaki uku ana gudanar da shi.