
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da daliban makarantar Gwamnati dake Dapchi da aka sace kuma aka dawo da su a makon nan. Shugaban ya gana da daliban ne ranar Juma’a a fadar Gwamnati dake birnin tarayya Abuja.
A yayin ganawa da daliban, Shugaba Buhari ya shaidawa daliban cewar kada wannan abin da ya faru da su ya sa su ja da baya akan abinda ya shafi karatun boko, yace kada su ji ko gezau akan abinda suka kudurce dangane da karatunsu.
SHugaba Buhari ya gana da daliban ne yau Juma’a ciki har da wani yaro. An saki daliban ne a ranar Laraba bayan da aka sace su a ranar 19 gawatan Fabrairu a makarantar sakandiren Gwamnati dake garin Dapchi a jihar Yobe.