
Shugaba Muhammadu Buhari ya halarci bikin cikar kasar Ghana shekaru 61 da samun mulkin kai, wanda aka yi yau a babban birnin kasar Accra. Shugaba Buhari dai shi ne kadai Shugaban da aka gayyata daga wata kasa zuwa wajen wannan biki, ana kuma sa ran Shugaba Buharin zai gabatar da jawabi a yayin wannan biki.