Home Kanun Labarai Shugaba Buhari ya kamo hanyar dawowa gida Najeriya

Shugaba Buhari ya kamo hanyar dawowa gida Najeriya

0
Shugaba Buhari ya kamo hanyar dawowa gida Najeriya

Fadar Shugaban kasa ta tabbatar da cewar, Shugaban kasa Muhammadu Buhari yanzu haka ya kamo hanyar dawowa gida Najeriya, bayan da ya yada zango a birnin Landan na kasar Burtaniya daga kasar Amurka.

Da yake magana da jaridar DAILY NIGERIAN ta wayar tarho, mai magana da yawun fadar Shugaban kasa Garba Shehu ya bayyana mana cewar, babu wani abin damuwa dangane da tsayawar Shugaba Buhari a birnin London.

“Babu wani abin tayarda hankali dangane da rashin isowar Shugaban kasa Najeriya kamar yadda aka tsara, abinda ya faru shi ne, Shugaban kasa yayi amfani da karamin jirgi nee, wanda yake bukatar samun hutu domin duba lafiyarsa”

“Jirgin da Shugaban kasa ya yi amfani da shi, baya jure doguwar tafiya, kuma kowa ya san daga Amurka zuwa Najeriya akwai nisa sosai, dan haka wannan jirgin yana bukatar a samu a dakata a idan anyi ‘yar tafiya da shi domin duba lafiyarsa”

“Yanzu haka Shugaban kasa ya baro birnin Landan zuwa Najeriya, bayan da aka gama duba jirgin nasa” A cewar Garba Shehu.

“It is just a routine stopover for safety checks during long journeys. Nothing strange in it.

“The president just left London for Nigeria after the aircraft underwent the routine check,” he added.