
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana nadamarsa kan rashin yin wasu muhimman naɗe naɗe a wasu hukumomin Gwamnati. Shugaban yayi wannan nadamar ne a ranar Talata, ya kuma sha alwashin cike duk wani giɓi a hukumomin Gwamnati nan da ɗan lokaci ƙanƙani.
Shugaban ya bayyana haka ne, a babban taron masu ruwa da tsaki da kuma shugabannin zartarwa na jam’iyyar APC da aka gudnar a fadar Gwamnati dake Abuja.
Shugaban a cikin jawabinsa ya tabo batutuwa da dama da suka shafi tafiyar Gwamnatinsa da kuma irin yadda mutane ke korafe korafe kan salon shugabancinsa, na rashin yin abubuwa da yawa cikin gaggawa.
Daga ciki ya fada cewar, “A shekarar da ta gabata, na shaida muku cewar, zamu yi naɗe naɗe a wasu hukumomin gwamnati da bamu yi ba tunda muka zo, sai dai kai gashi har yau bamu yi ba, sabida wasu dalilai, a wannan gabar, nake bayyanar muku da nadamata kan rashin yin wadancan naɗe naɗe na hukumomin Gwamnati”
“Wannan kuma ya faru ne, sakamakon sakaci da aka samu na kwamitin da na kafa wanda zasu duba wadan da suka dace dazamu naɗa a hukumomi daban daban, domin tafiya tare ba tare da nuna fifiko ga wani bangare ba”
“Ina sane da cewar, magoya bayanmu sun zaƙu da wadannan nade nade da suke jiran mu aiwatar da su,a sabida haka, ina mai tabbatar musu da cewar, zamu yi wadannan naɗe naɗe ba da jimawa ba, musamman yanzu da tattalin arziki ya farfado, muna da isassun kudade a hannu”
Sannan kuma, shugaban yayi godiya ga shugabannin jam’iyyar Musamman Cif John-Odigie Oyegun, da kuma jagoran jam’iyyar na kasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu, sannan kuma, shugaban yayi godiya ga majalisun dokoki na kasaa, musamman shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai Yakubu Doga akan irin gudunmawar da suke bashi.
Haka kuma, shugaban ya yi godiya ga dukkan ;ya ‘yan jam’iyyar ta APC bisa irin gudunmawar da suke baiwa jam’iyyar da kuma irin yadda suke baiwa jam’iyyar goyon baya.