
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja zuwa birnin Adis Ababa na kasar Ethiopia a ranar Juma’ah, a taroon kungiyar karo na 30 wanda Shugabannin kasashen duniya ke haduwa domin tattaunawa.
A taron karshe dai na kungiyar an dorawa Shugaba Buhari alhakin zamar da hanyoyin da za’a yaki cin hanci da rashawa a kasashen Afurka. Taron da akai wa take da sunan “Cin Nasarar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa” hanyar samun nasara.
Wannan dai shi ne karo na farko a cikin shekaru 54 da kafa kungiyar, da zata tattauna kan batn yaki da cin hanci da rashawa, a yankin nahiyar Afurka wanda dukkan Shugabannin nahiyar zasu halarta.
A taron kungiyar karo na 29 dukkan shugabanninkasashenduniya suka amince da nada Shugaba Buhari a matsayin wanda zai tattauna kan yadda za’a yaki cin hanci da rashawa.
Manyan jami’an Gwamnati ne ake sa ran zasu rufawa Shugaba Buhari baya zuwa wannan taron. Daga cikinsu akwai Ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau da Ministan harkokin jiragen sama, Hadi Sirika da mai baiwa Shugaban kasa shawara kan al’amuran tsaro Babagan Munguno.
Sauran sune, Ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama da Ministan Shariah kuna Antoni janar na kasa Abubakar Malami.
Sannan kuma da Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC, Ibrahim magu.