Home Labarai Shugaba Buhari zai yi balaguro zuwa kasar Maroko

Shugaba Buhari zai yi balaguro zuwa kasar Maroko

0
Shugaba Buhari zai yi balaguro zuwa kasar Maroko

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yi bulaguro a ranar Lahadinin nan zuwa kasar Maroko,inda zai kai wata zyara ta kwana biyu.

wannan ziyara dai, Shugaba Buhari ya same ta ne ta hanyar gayyatarsa da Sarkin kasar Maroko, Sarki Muhammad VI, ya yi masa.

Ana sa ran Shugabannin biyu zasu tattauna kan huldar kasuwanci tsakanin kasashen uda biyu, tun bayan da Sarkin ya kawo ziyara Najeriya a watan Disambar 2016 ne aka fara sanya dambar kulla alakar cinikayya tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Buhari zai yi wannan ziyara ne a babban birnin kasar wato Rabat, inda zasu tattauna batun shimfida bututun iskar gaz daga Najeriya zuwa kasar ta Maroko.