Home Kanun Labarai Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya sauƙa a birnin Kano a ziyarar da ya kai jihar ta yini biyu

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya sauƙa a birnin Kano a ziyarar da ya kai jihar ta yini biyu

0
Shugaban  ƙasa Muhammadu Buhari, ya sauƙa a birnin Kano a ziyarar da ya kai jihar ta yini biyu
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban  ƙasa Muhammadu Buhari ya sauka a birnin Kano da safiyar Laraba, a ziyarar da ya kai jihar ta yini biyu. Wannan daishi ne karon farko da Shugaban ya kai ziyara jihar ta Kano tun bayan zabensa da aka yi a matsayin Shugaban Najeriya a zaben 2015.

Kafin wannan ziyara da Shugaban ya kawo a yau, tuni, mutane da dama suka yi ta yin kiraye kiraye ga Shugaban da ya waiwayi jihar ta Kano. A cewarsu, tun bayan da aka zabe shi Shugaban kasa, bai waiwaye su ba.

An yi ta rade radin Shugaban zai kawo irin wannan ziyara a makon da ya gabata, wadda Shugaban bai zo ba, hakan ta harzuka wasu matasa da dama, har suka dinga bin tituna suna ciccire manyan allunan Shugaban da Gwamnatin Kano ta kafa a Daura da hanyar shiga gidan gwamnatin Kano.

Ana sa ran Shugaban, yayin wannan ziyara zai kaddamar da wasu manyan ayyuka da suka hada da Asibitin Giginyu da na kan titin zuwa gidan namun daji (zoo road) wanda aka gina shi zamanin tsohuwar gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau.

Sauran sun hada da aikin hanyar Panshekara da kuma aza harsashin gina sabuwar Kasuwar duniya a garin dan  gwauro, wadda itama aka faro aikin tun zamanin Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau.

An dai shirya, Shugaban zai gana da kungiyoyin ‘yan kasuwa da na Malamai da sauran al’umma a jihar Kanon a yayin wannan ziyara ta yini biyu da shugaban zai kawo.