Home Labarai Shugaban ƙungiyar Izala na ƙasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ƙaddamar da sabuwar makarantar a Yola

Shugaban ƙungiyar Izala na ƙasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ƙaddamar da sabuwar makarantar a Yola

0
Shugaban ƙungiyar Izala na ƙasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ƙaddamar da sabuwar makarantar a Yola
Shugaban kungiyar Izala na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau
A ranar litinin ne shugaban kungiyar Izala ta kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ya kaddamar da katafariyar makarantar Haddace Al-Qur’ani mai girma a Yola babban birnin jihar Adamawa, ita wannan makaranta Shugaban Izala ne da kansa ya gina ta da kansa.
Makarantar wadda ta samu kayataccen gini na zamani, an bude ta ne musamman saboda haddace Al-Qur’ani mai tsarki ga yara ‘yan shekara uku zuwa shekara shida, inda za’a basu horon haddace Al-Qur’ani mai girma a cikin shekaru uku 3 kacal.
An kuma tanadar da dukkan wani abu da dalibai zasu bukata, kama daga abinci zuwa masu yi musu hidima, tare da kwararrun Malamai da za su ba su karatun.
Ana sa ran makarantar zata zo da sabon salo da zai inganta yanayin yadda ake haddace al-qurani mai tsarki. Manyan malamai da jami’an Gwamnatin jihar Adamawa ne suka halarci bikin bude makarantar.