
A ranar Alhamis majalisar dokokin jihar Kano karkashin jagorancin Abdullahi Ata ta tantance Shugaban riko na jam’iyyar APC bangaren Gandujiyya Abdullahi Abbas a matsayin Kwamishina.
Idan ba’a mance ba, an samu wata mummunar baraka tsakanin Shugaban jam’iyyar Abdullahi Abbas da kuma Mataimakin Gwamnan Kano Farfesa Hafizu Abubakar, wadan da suka fito daga karamar hukumar Gwale.
An fara samun turka turka ne tsakanin Mataimakin Gwamnan da kuma Shugaban jam’iyyar, bayan da aka rushe Shugabancin mazabarMandawari da kuma karamar Shukumar Gwale na jam’iyyar ba tare da an tuntubi shi mataimakin Gwamnan ba.
A cewar mataimakin Gwamna Hafizu Abubakar, shugaban mazabar Mandawri da aka cire kaninsa ne uwa daya uba daya, aka cire don a bakanta masa rai, a fadi hakan a wata hirarsa da aka nada.
Ba tare da bata lokaci ba, bayan da kakakin majalisar ya gabatar da takardar da Gwamnati ta aikowa majalisar tana mai neman a amince da Abdullahi Abbas a matsayin Kwamishin. Mataimakin kakakin majalisar ne, yace abar Abdullahi Abbas kawai ya rusunawa majalisar ya wuce ba tare da an yi masa tambaya ko guda daya ba.
Bayan da aka tabbatar masa da cewar an amince da shi ya zama Kwamishina, Abdullahi Abbas yace, a shirye yake ya yi aiki tukuru a dukkan ma’aikatar da aka tura shi a matsayin kwamishina.
Haka kuma, a yayin zaman,majalisar ta amince da wasu wasiku guda biyu da Gwamnatin Kanon ta aiko mata, inda wasika ta daya, take neman sahalewar majalisar kan kasafin naira biliyan 174 ga ma’aikatar kananan hukumomi.
Yayin da wasika ta biyu, take neman sahalewar majalisar akan kasafin naira biliyan 5 ga masarautar Kano. Majalisar kuma ta amince da wannan bukata ta bangaren zartarwa.