
A jiya Litinin ne dai shugaban kamfanin kafar sadarwa ta Twitter, Jack Dorsey ya yi murabus da ga shugabancin kamfanin.
Ya wallafa sanarwar a shafinsa na twitter ɗin, inda hakan ya kawo ƙarshen shekaru 16 na shugabancin sa a matsayin wanda ya ke da hannun jari a kamfanin.
“Na yi murabus da ga twitter,” in ji shi.