Home Kanun Labarai Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ziyarar yini biyu a jihar Jigawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ziyarar yini biyu a jihar Jigawa

0
Shugaban kasa Muhammadu Buhari na ziyarar yini biyu a jihar Jigawa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau litinin ya kai ziyarar yini biyu a jihar Jigawa inda zai kaddamar da wasu manya manyan ayyukan raya kasa da bunkasa harkar noma da Gwamnatin jihar karkashin Gwamna Badaru Abubakar ta aiwatar.

Ana sa ran Shugaba Buhari zai kaddamar da aikin noman rani na zunzurutun kudi Naira biliyan tara a Hadejia dake jihar ta jigawa. Bayan nan kuma ana sa ran Shugaban zai kaddamar da ayyukan tituna da asibitoci da sauransu a yayin wannan ziyara tasa ta yini biyu.