
A ranar litinin dinnan, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar birnin tarayya Abuja, domin zuwa birnin Tahoua a jamhuriyyar nijar domin halartar bikin zagayowar ranar kafa kasar Nijar, kamar yadda wata sanarwa daga fadar Shugaban kasa ta nuna.
Shugaba Buhari tare da takwarorinsa na kasashen Mali da Burkina Faso da Chadi da Mauritaniya da kuma babban mai masaukinsu Shugaban Nijar Mouhammadou Isoufou, zasu halarci bikin mai dumbin tarihi wanda ake yinsa a dukkan 18 ga watan Disamba, domin tunawa da ranar da aka kafa Jamhuriyyar Nijar.
Bayan wannan kasaitaccen biki da za ai, Shugaban na Nijar zai yi wata tattaunawa ta musamman da Shugabannin kasashen da suka halarci taron tare da wata liyafa ta kasaita.
Shugaba Muhammadu Buhari zai halarci wannan taron bisa rakiyar Gwamnonin jihohin Katsina, Yobe da kuma Borno, wato Aminu Bello Masari da Ibrahim Geidam da kuma Kashim Shetima, ana sa ran Shugaban zai dawo a yau litinin bayankammala taron.