Home Labarai Shugaban Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci, Dakta Ahmad ya rasu

Shugaban Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci, Dakta Ahmad ya rasu

0
Shugaban Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci, Dakta Ahmad ya rasu
Shugaban Majalisar Ƙoli ta Shari’ar Musulunci a Nigeria Dakta Ibrahim Datti Ahmad ya rasu a jiya Laraba.
 A wata sanarwa da jaridar KANO FOCUS ta samu, an baiyana cewa za a yi jana’izar marigayin a Masallacin Al Furqan, a yau Alhamis da ƙarfe 10 na safe.
Marigayi Dr Ahmad yana ɗaya daga cikin jerin likitoci na farko ‘yan asalin Jihar Kano.
Marigayin mutum ne mai kishin addinin Musulunci. Wanda ya sha yin korafi kan yadda ake zaluntar sojoji musulmi a Nijeriya da kuma yadda ake musgunawa Musulmi baki ɗaya.
Tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya taɓa naɗa shi cikin jerin mutanen da za su jagoranci tattaunawa da ‘yan Boko Haram kafin daga baya ya fice daga cikin shirin.
Ya kuma taɓa neman zama dan takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam’iyyar SDP.
Haka-zalika sunan marigayin ya taɓa fitowa a cikin jerin shahararrun Musulmi 500 a duniya.