Home Siyasa Shugaban PDP ya yi suɓutar-baki a Kano

Shugaban PDP ya yi suɓutar-baki a Kano

0
Shugaban PDP ya yi suɓutar-baki a Kano

Shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Iyorcha Ayu, a jiya Alhamis ya yi suɓutar-baki a lokacin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar a Kano.

Yayin da ya ke nufin jam’iyyar APC, Ayu cikin kuskure ya bukaci masu zabe su yi watsi da jam’iyyar PDP saboda ta jefa kasar nan ciki halin kunyata a duniya.

Ya ce: “Ya kamata mu zama shugabanni a Afirka, da kuma ko’ina a duniya, amma PDP ta jawo mana kunya kuma ba za mu bar ta ta ci gaba da rike mulki ba.” In ji Ayu, yayin da ya ke nufin APC.

Daga nan ya bukaci jama’a da su zabi PDP daga sama har kasa.

A tuna cewa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Atiku Abubakar shi ma ya yi irin wannan suɓutar-baki a cikin watan Disamba a lokacin yakin neman zaben jam’iyyar a Jos.

Dan takarar jam’iyyar PDP, a lokacin da yake jawabi ga dimbin jama’a a filin wasa na Rwang Pam a garin Jos, ya ce: “Don Allah da darajar wannan wuri, ku tabbatar kun zabi AP, ina nufin PDP, a wannan karon”.