
Shugaban majalisar dokokin Sri Lanka ya bayyana cewa Shugaba Gotabaya Rajapaksa zai sauka daga mulki ranar Laraba 13 ga watan Yuli.
Wannan ya biyo bayan gagarumar zanga-zanga da aka yi tsawon rana a yau da kuma zaman tattaunawa tsakanin shugaban majalisar da firaministan kasar da kuma shugabanin jam’iyya.
Bukatar shugaban ya sauka daga mulki dai ita ce gaba-gaba da masu zanga-zangar ke nema tsawon watanni saboda gazawar hukumomi na magance hauhawarar farashi da karancin abinci da man fetur da kuma magani.
A yau Asabar, masu zanga-zangar suka kwace iko da gidan shugaba Rajapaksa, inda daga bisani suka cinna wa gidan firaministan kasar, Ranil Wickramasinghe wuta.