
A wani yanayi na bazata, ƴan takara uku da ke neman Shugabancin Majalisar Wakilai ta 10 mai jiran gado, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar, Alhassan Ado Doguwa, Abdulraheem Olawuyi da Abubakar Makki Yelleman sun ajiye takarar su donin goyon bayan dan takarar da jam’iyyar APC ta zaɓa, Tajuddeen Abbas.
Sun bayyana matakin nasu ne a taron hadin gwiwa na majalisar ta 10 da aka yi a Abuja a daren jiya Laraba.
Taron ya samu halartar shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila da dan takarar shugaban majalisar dattawa ta 10, Sanata Godswill Akpabio.
“Doguwa wanda ya yi magana a madadin sauran ƴan takarar biyu ya ce, sun yanke shawarar ficewa ne domin su mutunta zabin jam’iyyar APC tare da yin daidai da wanda ake so a kujerar Shugaban Majalisar.
“Masu girma, na zo ne in shaida muku cewa, ba wai daga yau ba, tun a ranar farko, da kwamitin ƙoli na jam’iyyata ta kasa ta dora a kan teburi cewa, za a bi tsarin shiyya-shiyya ta fitar da shugabancin majalisar tarayya.
” Kuma gashi tsarin ya taho Arewa maso Yamma sannan ai baiwa dan uwa na, Right Honourable Tajuddeen Abbas mai wakiltar mazabar tarayya ta Zariya daga Arewa maso Yammacin Najeriya, tun daga wannan lokaci, don haka na dakatar da yunkurina na tsayawa takarar shugaban majalisar wakilai ta 10,” in ji Doguwa.