Home Siyasa Shugabannin APC na Doguwa sun kai wa Garo ziyarar dannar-ƙirji

Shugabannin APC na Doguwa sun kai wa Garo ziyarar dannar-ƙirji

0
Shugabannin APC na Doguwa sun kai wa Garo ziyarar dannar-ƙirji

 

Shugabanni da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC sun kai ziyarar bada hakuri mataimakin ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a Kano, Murtala Sule Garo.

A jiya Talata ne jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa an samu saɓani tsakanin Garo da Alhassan Ado Doguwa, Shugaban Masu Rinjaye na Majalisar Wakilai.

Jaridar ta rawaito cewa har ta kai ga Doguwa ya jefi Garo da kofin shayi, inda har ya ji masa rauni a yayin wani taron masu ruwa da tsaki na APC a gidan Mataimakin Gwamnan Kano, Dakta Nasiru Yusuf Gawuna a ranar Litinin.

Sai dai kuma Doguwa, a ta bakinshi, ya amince da cewa sun samu saɓani da Garo, amma bai ji masa ciwo ba.

Sai dai kuma a yau Laraba, wasu hotuna su ka fara karade kafafen sadarwa, inda a ka ga manyan jam’iyyar na Doguwa a gidan Garo, a wani yanayi na ziyarar dannar-ƙirji a kan abinda ya faru.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa tabbas an kai ziyarar a yau Laraba a gidan Garo da ke jihar Kano.

Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa ne ya jagoranci tawagar tare da ɗan majalisar jiha mai wakiltar Doguwa, Salisu Mohammed da tsohon kwamnishina Usman Sule Riruwai.

Sauran ƴan tawogar sun haɗa da mataimakin shugaban Jam’iyya, Shehu Maigari, da shugaban Ƙaramar Hukumar Doguwa, Alhaji Mahmuda Hudu da Shugaban Jam’iyyar APC na Doguwa da sauran jagororin Jam’iyya.

Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa shugabbannin sun yi bayani na nuna rashin jin dadi.

Sun kuma roƙi Garo da ya yi hakuri sannan su ka tabbatar da za su ɗauki matakin da ya dace tun daga tushe.