Home Siyasa Shugabannin jam’iya na mazaɓa kawai kotu ta rushe a Kano – Gwamnati

Shugabannin jam’iya na mazaɓa kawai kotu ta rushe a Kano – Gwamnati

0
Shugabannin jam’iya na mazaɓa kawai kotu ta rushe a Kano – Gwamnati

 

Gwamnatin Kano ta ce hukuncin da wata babbar kotu ta yanke a Abuja, wanda ta rushe shugabannin jam’iya mai mulki ta APC a Kano ya shafi shugabannin mazaɓa ne kawai ba na ƙananan hukumomi da na jiha ba.

Daily Nigerian Hausa ta rawiato a yau talata cewa kotun, ƙarƙashin jagorancin Hamza Muazu ta rushe zaɓen shugabancin jam’iyar APC da tsagin gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ya gudanar.

Haka kuma mai shari’ar ya tabbatar da zaɓen da tsagin tshohon gwamnan Kano Ibrahim shekarau ya gudanar.

Da ya ke martani a kan hukuncin kotun, Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ya ce har yanzu uwar jam’iya ta ƙasa shugabannin jam’iya na ɓangaren gwamma Abdullahi Ganduje ta sani.

A wata sanarwa da ya fitar, Garba ya ce tuni lauyoyin jam’iyar su ka shirya takardu domin shigar da ɗaukaka.

Ya ce za su je kotun ɗaukaka ƙara ne don ƙalubalantar hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke.

Garba ya yi kira ga ƴan jam’iyyar da su kwantar da hankulansu su ci gaba da gudanar da ayyukansu kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada.