
Rundunar Sibil Difens, NSCDC ta tabbatar da kama wasu ƴan ta’adda masu fashin daji waɗanda su ka tsere da ga Magami, a Jihar Zamfara sakamakon hare-haren da a ke kai musu.
Kakakin NSCDC, Ikor Oche ne ya tabbatar da kamen a taron manema labarai, inda ya ce an kama ƴan ta’addan ne a tashar motar kamfanin sufuri na Zamfara da ke Gusau a jiya Litinin.
A cewar Oche, an cafke ƴan ta’addan ne da sassafe yayin da su ke ƙoƙarin guduwa zuwa Jihar Taraba domin haɗuwa da ƴan uwansu da su ka riga su ka gudu can.
Ya ce da ga cikin su akwai Tukur Halilu ɗan shekara 27 ɗan asalin ƙauyen Gabaru a garin Nahuce da ke Ƙaramar Hukumar Bagudu, wanda ya ke a ƙarƙashin wani ƙasurgumin ɗan fashin daji, mai suna Magajin Kaura.
A cewar sa, Halilu ya tabbatar da cewa ya aikata satar shanu da dama a ƙauyuka da dama yankin karamar hukumar.
Oche ya ƙara da cewa sauran sun haɗa da Hussaini Altine mai shekara 40 sai kuma Abubakar Altine mai shekara 60 dukkan su ƴan ƙauyen Agamalafiya ne a unguwar Rijiya a ƙaramar hukumar Gusau.
“Duk da dai Abubakar Altine ya nuna shi ba ruwan sa, Hussaini ya tabbatar da cewa shi a ƙarƙashin wani ƙasurgumin ɗan fashin daji Gugurawa ya ke,” in ji shi.
Kakakin ya ce da Hussaini Altine a ka kai hare-hare guda uku a ƙauyukan Kurya, Bagawuri, Agamalafiya da Rijiya.
Ya ƙara da cewa ana nan ana yin bincike mai zurfi a kan su wanda hakan zai sanya a iya kama wasu da ga cikin su.