Home Labarai Siyasar Kano: Wasu na hannun daman Shekarau sun koma Kwankwasiyya

Siyasar Kano: Wasu na hannun daman Shekarau sun koma Kwankwasiyya

1
Siyasar Kano: Wasu na hannun daman Shekarau sun koma Kwankwasiyya
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tsohon Gwamnan kano

Tuni dai kurar siyasa ta fara turnukewa a jihar Kano, tsakanin manya manyan ‘yan siyasar jihar. Domin kuwa wasu jigajigan mutane da ke tare da tsohon Gwamna Ibrahim Shekarau sun balle sun koma Kwankwasiyya.

Malam Abdullahi Sani  Rago da Salisu Gwangwazo da aka fi sani da Alhajin Baba da Ali Datti Yako, sun kulla auren siyasarsu da tsohon Gwamna Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

KO a kwanakin baya dai sai da wani na kusa da Malam Shekarau mai suna Musa Iliyasu Kwankwaso ya balle ya koma jikin Gwamna mai ci Abdullahi Umar Ganduje.

A ranar Juma’ar da ta gabata, Rogo da Yako da Gwangwazo sun jagoranci wasu gaggan ‘yan PDP inda suka je suka zauna da Sanata Kwankwaso, inda suka bayyana cikakken goyon bayansu ga Kwankwasiyya.

Wata majiya a yayin wannan tattaunawa ta shaidawa DAILY NIGERIAN cewar, mutanan sun tabbatarwa da Kwankwaso cikakken goyon bayansu ga tafiyar kwankwasiyya.

Mutanan da suka marawa su Rogo baya zuwa tafiyar Kwankwasiyya sun hada da, Dankaka Usaini Bebeji, Muktari Dankadai, Muazzam Madobi da Bello Bichi wanda dukkaninsu tsaffin Shugabannin kananan hukumomin jihar Kano ne karkashin Gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau.

A lokacin da yake maida martani dangane da wannan ziyara tasu, Salisu Gwangwazo, ya tabbatarwa da Daily Nigerian cewar “Wannan ziyara ba komai bace face kokarin hada hannu da karfe wajen kayar da Ganduje”

“Sanata Kwankwaso jigo ne a siyasar jihar Kano, kuma duk wanda yake adawa kuma yake fatan ya kafa Gwamnati to tilas ya nemi goyon bayansa”

Su dai su, Abdullahi Sani Rago sun ga take taken Malam Ibrahim Shekarau ne cewar kamar ba zai marawa Malam Salihu Sagir Takai baya ba a zaben 2019 dake tafe.