Home Labarai Sojoji sun hallaka rikakken ɗan ta’adda, Halilu Sububu da mayakan sa a Zamfara

Sojoji sun hallaka rikakken ɗan ta’adda, Halilu Sububu da mayakan sa a Zamfara

0
Sojoji sun hallaka rikakken ɗan ta’adda, Halilu Sububu da mayakan sa a Zamfara

Rahotanni daga jihar Zamfara na nuni da cewa sojojin Najeriya sun hallaka Halilu Sububu, dan ta’adda da ya yi kaurin suna a yankin Arewa maso Yamma.

Sububu, wanda ya kwashe shekaru ya na ta’addanci a jihar Zamfara, ya gamu da ajalin sa a jiya Alhamis.

Wata majiyar asiri ta tsaro a safiyar yau Juma’a ta tabbatar da kisan dan ta’addan da sojoji su ka ga jaridar PRNigeria.

“A wani samame da dakarun soji suka kai jiya, sun yi nasarar hallaka shahararren dan bindigar nan Halilu Sububu tare da wasu ‘yan bindiga da dama a Zamfara a daren jiya.

“Sojoji sun kuma kwato muggan bindigogi da alburusai, tare da babura daga hannun ‘yan ta’adda,” in ji majiyar.