
Yan ta’adda da dama da ake zargin mayakan ISWAP ne sun gamu da ajalinsu a hannun sojojin Najeriya bayan da suka yi yunƙurin kubutar da shugabanninsu a wani sansanin tsaro da ke New Bussa a jihar Neja.
Wata majiyar sirri ta tsaro ta shaidawa PRNigeria cewa sojoji sun daɗe suna hasashen ƴan ta’addan, inda kuwa su ka yi musu kwanton-ɓauna.
“Ko da ya ke lamarin ya faru ne da daddare, sojojin sun yi ta hasashen za a yi hakan kuma sun kasance cikin shiri.
“Sun shigo tarkon mu ne kawai. Yayin da aka kirga gawarwakin ‘yan ta’adda akalla bakwai a safiyar yau. Sojojin sun yi nasarar cafke daya daga cikin kwamandojin su da ya jagoranci mayakan.
“Jigin sama na NAF sun kuma kasance a kan lokaci wajen tallafawa sojojin kasa daga gundumar bataliyar Wawa a Ƙaramar Hukumar Borgu ta jihar Neja, don haka an samu nasarar kakkabe ‘yan ta’adda,” in ji shi