Home Labarai Sojoji sun kashe ɗan fashin daji 1 tare da kama 3 a Kaduna

Sojoji sun kashe ɗan fashin daji 1 tare da kama 3 a Kaduna

0
Sojoji sun kashe ɗan fashin daji 1 tare da kama 3 a Kaduna

 

 

Dakarun runduna ta 1 ta Rundunar Sojojin Ƙasa sun kashe wani dan fashin daji tare da cafke wasu guda uku da ake zargi a Kaduna a jiya Litinin.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ne ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai a yau Talata a Kaduna.

A cewar sanarwar, sojojin sintiri na yaki, ƙarƙashin jagorancin babban kwamandan rundunar, GOC, shiyya ta ɗaya ta sojojin Najeriya, Manjo-Janar Taoreed Lagbaja, tare da tawagar kwamandojin aiki ne su ka samu nasarar kama ƴan ta’addan.

“Jami’an tsaro sun fatattaki ƴan bindiga a garuruwan Buruku, Udawa, Manini, Birnin Gwari, Doka, Maganda, Kuyello da kuma Dogon Dawa a jihar Kaduna, yayin da suke sintiri a jiya Litinin.

“A yayin da ake musayar wuta a lokacin gudanar da aikin, rundunar ƴan sintiri ta yi galaba a kan ƴan bindigar da karfin wuta, inda suka kashe daya daga cikinsu, yayin da aka kama wasu uku da ransu, sannan wasu daga cikin ƴan ta’addan suka tsere da raunukan harbin bindiga.

Nwachukwu ya ce rundunar ta kuma kwato bindiga kirar AK 47 guda daya, harsashi na musamman mai girman 7.62 mm 7.62 da kuma babura 18.