Home Labarai Sojoji sun kashe gwanin haɗa bam na ƙungiyar ISWAP tare da mayaƙa 3 a Borno

Sojoji sun kashe gwanin haɗa bam na ƙungiyar ISWAP tare da mayaƙa 3 a Borno

0
Sojoji sun kashe gwanin haɗa bam na ƙungiyar ISWAP tare da mayaƙa 3 a Borno

 

 

 

Rahotanni sun bayyana cewa, dakarun runduna ta 25 ta ‘Operation Hadin Kai’ sun kashe mayakan kungiyar ISWAP hudu, ciki har da Modu Tafjid, gwanin haɗa bama-bamai a ƙauyen Kumala dake kan hanyar Maiduguri zuwa Damboa, a jihar Borno.

A cewar Zagazola Makama, wani kwararre mai sharhi kan fannin yaki da ta’addanci a yankin tafkin Chadi, mayakan ISWAP sun yi wa sojojin kwanton-bauna, inda su kuma sojojin, tare da rundunar haɗin gwiwa ta ‘Civilian Task Force’ su ka daƙile harin.

Majiyoyi sun ce mayakan na ISWAP sun tayar da bam a kan ɗaya daga cikin motocin sintiri na sojojin wanda ya biyo bayan harbin bindiga.

Wata majiya ta ce sojojin sun yi artabu da mayakan na ISWAP a wani kazamin artabu amma suka fatattake su.

“Modu Tafjid, kwararre wajen haɗa bam, da ya jagoranci harin da wasu ’yan ta’adda guda uku an kashe su a sakamakon artabun, yayin da wasu ‘yan ta’adda da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga,” inji Makama.

Wannan ci gaban dai na zuwa ne kwanaki bayan da aka kashe mayakan Boko Haram da ISWAP da dama a wani hari ta sama da sojojin saman Najeriya suka kai a karamar hukumar Bama ta jihar Borno.