
Dakarun Sojojin Nijeriya da ke Birged ta2 tare da hadin guiwar ƴan sanda da jami’an tsaron farin kaya da na rundunar kare fararen hula, NSCDC da sauran jami’an tsaro sun kashe shugaban wata kungiyar ƴan daba mai suna Otobong Moses, da a ke masa laƙabi da Otoabasi a wani sumame da suka kai maɓoyar su a Akwa Ibom.
Mataimakin Daraktan Hulda da Jama’a na Sojojin Najeriya na runduna ta 2 ne ya bayyana haka ga manema labarai bayan wani samame da suka kai a Obon Ebot a Ƙaramar Hukumar Etim Ekpo a jihar.
Akari ya ce sojojin sun kame uku daga cikin wadanda aka hada baki a ke aikata laifuka, tare da kubutar da wasu mutane biyu da aka yi garkuwa da su a yayin sumamen.
Ya bayyana cewa kayayyakin da aka kwato daga samamen sun hada da bindigogi iri-iri da mazubabn harsashi, harsashai 67 mai tsayin 9MM, babura biyu, wayoyin hannu 16, mazubin harsashin bindiga kirar AK 47 daya da harsashi na musamman 7.62MM guda 30 da adduna tara.
Ya kara da cewa, sauran kayayyakin da aka kwato sun hada da rigunan biri guda biyu na soja, hula guda daya sanye da kakin soja, da kakin soja guda 2, da katin soja guda daya, katin ATM, Talabijin guda biyu, fanfo na tsaye, dikodar da injin janareta hudu.