
Dakarun runduna ta 5 ta sojojin Najeriya sun kaddamar da gagarumin farautar ‘yan ta’addar Boko Haram/ISWAP da ke ta’addanci a yankin Damasak na jihar Borno.
Sojojin da ke sintiri na yaki sun yi arangama da ‘yan ta’addan ne a ranar Asabar, inda su ka yi nasarar kutsawa maɓoyar su.
Wannan bajintar wanda da alama an yiwa ‘yan ta’addan kwanton-ɓauna ne, shi ya sanya ‘yan Boko Haram/ISWAP su ka yi watsi da manyan makamansu su ka tsere.
Rundunar sojin Najeriya ta baiyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter a ranar Lahadi.
A cewarsa: “Dakarun Runduna ta 5 da ke sintiri a yankin BHT/ISWAP da ke Douro kusa da Damasak a Jihar Borno a ranar Asabar 29 ga watan Janairu, sun kutsa cikin wurin ‘yan ta’addan. A yayin harin ‘yan ta’addan sun tsere cikin rudani inda suka yi watsi da manyan bindigogi da makamansu. A halin yanzu ana ci gaba da sintiri mai tsanani,”