
Sojojin Najeriya sun kama wasu maƙudan kuɗaɗen fansa da za a kai domin sakin wasu da ƴan fashin daji a ke tsare da su a Jihar Kaduna.
PRNigeria ta jiyo cewa a na kyautata zaton wasu daga cikin masu kai kuɗin fansar jami’an tsaro ne.
Sojojin da ke aikin soja na leken asiri sun kuma ceto wadanda aka yi garkuwa da su da suka hada da wasu mata da kananan yara.
Sumamen, wanda a ka yi shi abinda ya da sojojin ƙasa da da kuma wata rundunar sojin sama ta musamman, NAF ya bada damar nasarar fatattakar wasu ƴan ta’addan.
Wani jami’in leken asiri ya shaidawa PRNigeria cewa dakarun NAF Detachment na 271 a Birnin Gwari, da dakarun sojojin Najeriya na FOB a Gwaska, sun kubutar da dimbin mutanen da aka yi garkuwa da su a yayin gudanar da aikin na hadin gwiwa.
Jami’in ya ce: “An kwato tsabar kudi naira miliyan 60,000,000, man fetur da kuma muggan makamai, a yayin gudanar da aikin.
“Sauran kayayyakin da sojojin suka kwato daga hannun wadanda ake zargin sun hada da motoci, bindigogi kirar AK-47, mujallu, harsashai iri-iri da wayoyin hannu.
“A halin da ake ciki, za mu mika karar ‘yan aike da aka kama wadanda akasarinsu ke da shaidar jami’an tsaro zuwa ga hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da hukumar leken asiri ta tsaro (DIA) domin ci gaba da bincike.”