
Dakarun sojin Najeriya da ke aiki da runduna ta 14 da ke Ohafia sun kai samame wani gidan da ake zargi ana ajiye mata don su haihu a sayar da jariran a unguwar Umunkpei Nvosi ta yankin ƙaramar hukumar Ngwa ta jihar Abia da ke kudu maso gabashin ƙasar.
BBC Hausa ta rawaito cewa sojojin sun samu nasarar kuɓutar da mata 22, waɗanda 21 daga cikinsu ke da juna biyu, ciki har da jarirai biyu.
Sauran abubuwan da aka samu a cikin gidan sun haɗar da injin bayar da wutar lantarki da tukunyar gas, da buhun shinkafa, da man girki da buhun garin kwaki biyu da sauran abubuwa.
Jami’an tsaron sun ce sun kai samamen ne bayan da suka samu bayanan sirri, cewa wadda ta mallakin gidan na sayar da jarirai ga wasu mutanen domin aikata tsafi, da masu safarar yara.
Ana zargin cewa matar ta ɗauki lokaci tana aikata laifin a yankin bayan da aka riƙa ganin sassan jikin mutane a kusa da ginin gidan.
Wani daga cikin dakarun sojin ya ce matar da ta mallaki gidan ta tsere a lokacin samamen, sai dai ya ce ana ƙoƙarin kama ta.
Tuni jamai’an tsaron suka miƙa matan da suka kuɓutar tare da jariran zuwa hannun gwamnatin jihar Abia domin ɗaukar mataki na gaba.