Home Kanun Labarai Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan Boko Haram 7 da kama motoci 12

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan Boko Haram 7 da kama motoci 12

0
Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan Boko Haram 7 da kama motoci 12

Rundunar sojojin Najeriya, ta ci nasarar murkushe wasu ‘yan kungiyar Boko Haram su 7 a dajin Sambisa dake Arewacin jihar Borno a ranar Juma’a a sakamakon wata batakashi da aka yi da su da sojojin sama.

A cewar wata sanarwa, daga Sani Usman, daraktan yada labarai na rundunar sojojin, wadda ya fitar a ranar juma’a da maraice, yace sojojin sunci nasarar tarwatsa wasu manyan motoci masu ruwan wuta goma sha daya  da kame motar Akuri-kura kirar Hilux guda sha biyu a yayin wannan artabu.

Mista Usman, ya bayyana cewar, daga cikin irin abubuwan da aka tarwatsawa ‘yan ta’addar sun kunshi gidan zama na tafi-da-gidanka, da kayayyakin fashewa da sauran kayayyaki masu matukar hatsari.

“Haka kuma, sojojin Najeriya sun ci nasarar kwato wata katuwar mota mai aman wuta daga nesa, da kuma wani makami mai linzami, da wata labarba, dakaramar bindiga ta hannu, tarin albarusai da kuma bindigogi kirar gida” A cewarsa.

“Sai dai, abin takaici, an jikkata mana sojojiguda iyu a yayin wannan artabu”

“Tuni dai aka dauke sojojin da suka ji ciwo, zuwa sansanin sojan sama domin samun kulawar gaggawa”

Ya cigaba da cewar, Kwamandan runduna ta 7, da manyan sojoji 27, Manjo Janar I. M. Yusuf, da Manjo Janar I. M. Obot, duk sun ziyarci sojojin da suka ji rauni kuma sun jinjina musu a madadin Shugaban hafsan tsaron Najeriya baki daya Tukur Buratai akan wannan muhimmin aiki da suka yi.

Sani Usman ya bukaci al’ummar jihogin Borno da Yobe da Adamawa da sukai rahoton duk wani dan Boko Haram da suka gani a yankinsu.

Sannan ya bukaci da su dinga sanya idanu ko zasu gano ‘yan ta”addar da aka jiwa raunuka, dan su kai rahoto zuwa ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa.

NAN