Home Labarai Sojojin Nijeriya sun hallaka ƴan ISWAP 21 a Borno

Sojojin Nijeriya sun hallaka ƴan ISWAP 21 a Borno

0
Sojojin Nijeriya sun hallaka ƴan ISWAP 21 a Borno

 

 

Akalla ƴan ta’addar ƙungiyar ISWAP/Boko Haram 21 ne suka mutu sakamakon harin bam da sojoji suka kai musu a yankin tafkin Chadi da ke jihar Borno.

Wani rahoto da jaridar PRNigeria ta fitar ya bayyana cewa, an hallaka da ƴan ta’addan ne a ranar Talata da wasu jirage masu saukar ungulu na yaki na rundunar Sojin Saman Nijeriya, NAF.

Wata majiyar leken asiri ta soji, a yayin da take tabbatar da harin da jiragen NAF suka kai wa ‘yan ta’addan, ta lura da cewa, an kuma lalata maɓoyar ƴan ta’addan a farmakin da suka kai na kwanan nan a Tumbun Jaki da Tumbun Murhu.

Majiyar ta ce: “Nasarar da aka samu ta kai hare-hare ta sama da aka gudanar a ranar 11 ga watan Yulin 2022 ta samo asali ne daga sahihan bayanan sirri kan ayyukan ƴan ta’addan a wuraren da aka ambata da kuma mayar da martani ga hare-haren da sojoji suka kai a yankunan Damasak da Mallam Fatori.

“A wani harin da aka kai tare da hadin guiwa ta hanyar amfani da kafafan yada labarai da sauran hanyoyin sadarwa na rundunar sojojin saman Najeriya, an ga maharan suna ta guduwa ta bangarori daban-daban, suna tururuwa domin tsira da rayukansu yayin da aka kai wa matsugunin su hari cikin gaggawa har a ka ƙona sansanonin su da maɓoyar kayan aikinsu.

“Wasu daga cikin mayakan Boko Haram na ISWAP da suka yi nasarar tserewa daga harin bam domin buya a duhuwa , inda daga baya a ka riƙa musu ruwan bama-bamai da rokoki.

“Bayanai da aka samu daga jami’an tsaro na kasa sun nuna cewa sama da ‘yan ta’adda 21 ne aka kashe a harin da aka kai ta sama,” in ji majiyar.