Home Labarai Sojojin Nijeriya sun hallaka ƴan IPOB 2 a Imo

Sojojin Nijeriya sun hallaka ƴan IPOB 2 a Imo

0
Sojojin Nijeriya sun hallaka ƴan IPOB 2 a Imo

 

Dakarun sojin Nijeriya sun kashe wasu ƴan kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra, IPOB da kuma kungiyar tsaro ta Gabas, ESN a Ƙaramar Hukumar Orsu ta jihar Imo su biyu dauke da makamai.

Daraktan hulɗa da jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba a Abuja.

Nwachukwu ya ce sojojin na Bataliyar sojin ƙasa ta 34, tare da hadin gwiwar sojojin ruwa, sojojin sama da sauran jami’an tsaro sun rufar wa masu laifin a jiya Talata a kan hanyar Eke Ututu-Ihitte Nansa.

Ya ce sojojin sun ci karo da ‘yan ta’addan ne a lokacin da su ke wani samame a kewayen yankin baki ɗaya.

A cewarsa, ƴan kungiyar da aka kashe sun ɗauki matakin harba makamin roka ɗaya a lokacin da sojoji kuma su ka rufar musu har su ka zaƙulo su.

“gwarazan dakarun ba su ji rauni ba ko ɗaya ba, yayin da wasu bama-bamai da ‘yan bindigar suka dasa a kasuwar Eke Ututu su ka yi bindiga, inda suka lalata wasu shaguna a kasuwar.