Home Labarai Sojojin Nijeriya sun kama ‘ƙasurguman ƴan fashi’ a jihohi 3 na Arewa

Sojojin Nijeriya sun kama ‘ƙasurguman ƴan fashi’ a jihohi 3 na Arewa

0
Sojojin Nijeriya sun kama ‘ƙasurguman ƴan fashi’ a jihohi 3 na Arewa

 

 

 

 

Rundunar sojan Najeriya ta ce ta yi nasarar kama ƙasurguman ‘yan fashin daji bakwai da masu taimaka musu a jihohin Kaduna da Filato da Nasarawa da ke arewacin ƙasar.

Wata sanarwa da Manjo Janar Benard Onyeuko ya sanya wa hannu ranar Juma’a ta ce dakarun rundunar sun yi nasarar ce cikin mako guda ta hanyar aikin haɗin gwiwa da mutanen gari da kuma bayanan sirri.

Daga cikin waɗanda aka kama akwai Danladi Selfa mai shekara 23 da Usman Yau mai 28 a Ƙaramar Hukumar Logo ta Jihar Nasarawa bayan an raunata su sakamakon fafatawar da suka yi da dakaru.

Haka nan, an kama Moses Aindigh mai shekara 27 da IIiyasu Mohammed mai 37, su ma a Nasarawa.

A cewar rundunar, a ranar 3 da 4 ga watan Agusta aka kama ƙasurguman ‘yan fashi – Umar Zakari, Usman Hamina, Haruna Umaru – a Jihar Kaduna.

Dakarun sun kuma yi nasarar kashe Umar Mohammed da ake zargi da garkuwa da mutane a Ƙaramar Hukumar Qua’anpan ta Jihar Filato a ranar 3 ga Agsuta.

Har wa yau, sojojin sun kuɓutar da Ebuka Nnadi mai shekara 30 da kuma Uchenna Edoga mai 25, waɗanda aka yi garkuwa da su a Gindiri na Ƙaramar Hukumar Mangu ta Filato ɗin.