Home Labarai Sojojin Nijeriya sun ce sun kama waɗanda ake zargi da harin cocin Owo a jihar Ondo

Sojojin Nijeriya sun ce sun kama waɗanda ake zargi da harin cocin Owo a jihar Ondo

0
Sojojin Nijeriya sun ce sun kama waɗanda ake zargi da harin cocin Owo a jihar Ondo

 

 

 

Shelkwatar tsaro ta bayyana cewa ta samu nasarar cafke ‘yan ta’addan da suka kai hari a cocin St. Francis Catholic Church da je garin Owo, a jihar Ondo.

Babban Hafsan Sojojin Najeriya Janar Lucky Irabor ne ya sanar da hakan a ranar Talata, a wani taro da shugabannin kafafen yada labarai a shedikwatar tsaro da ke Abuja.

Jaridar The Nation ta rawaito cewa Irabor ya ce an kama masu laifin ne tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro.

Kimanin mutane 40 ne suka mutu a lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari cocin a ranar 5 ga watan Yuni, inda suka bude wuta kan jama’ar, sannan kuma suka tayar da bama-bamai a yayin da masu ibada suka gudu domin tsira da rayukansu.