Home Labarai Sojojin sama sun hallaka shugaban ƴan ta’adda, Alhaji Shanono da mayaƙansa 17 a Kaduna

Sojojin sama sun hallaka shugaban ƴan ta’adda, Alhaji Shanono da mayaƙansa 17 a Kaduna

0
Sojojin sama sun hallaka shugaban ƴan ta’adda, Alhaji Shanono da mayaƙansa 17 a Kaduna

 

 

Rundunar sojin saman Najeriya, NAF,  ta ce ta kashe shugaban ‘yan bindiga Alhaji Shanono da wasu 18 a Kaduna.

Kakakin NAF, Edward Gabkwet ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a jiya Laraba.

Ya bayyana cewa an kashe ‘yan bindigar ne biyo bayan ci gaba da kai samame a yankin Arewa maso Yamma. A cewarsa, an kubutar da mutane akalla 26 da ‘yan ta’addan suka yi garkuwa da su bayan harin da aka kai ta sama.

Ya kara da cewa babban hafsan sojin sama, Oladayo Amao, ya yabawa sojojin bisa ci gaba da kai hare-hare ta sama kan ‘yan bindiga da ke aiki a yankin.

“Daya daga cikin irin wadannan hare-haren, wanda ya faru a ranar 9 ga watan Agusta, ya yi sanadin kawar da wani fitaccen shugaban ‘yan ta’adda da ke aiki a jihar Kaduna. Hakika, bayan samun bayanan sirri a wannan rana, cewa wani fitaccen sarkin ‘yan tada kayar baya, Alhaji Shanono, ya shirya ganawa da sojojin sa na kafarsa a Ukambo, wani kauye mai tazarar kilomita 131 daga Kaduna.” Inji sanarwar NAF.

Ya kara da cewa, “Sashin jirgin sama na Operation ‘Whirl Punch’ ya aika da jirgin sama don yin katsalandan a wurin. Gaba da wurin, an ga maharan a karkashin gungun bishiyoyi a gindin babban filin Ukambo, kuma bayan tabbatar da cewa babu fararen hula a wurin, ma’aikatan jirgin sun samu izinin kai farmaki.”

A cewar sanarwar, wasu bayanai da aka samu daga majiyoyin kasar sun bayyana cewa an lalata sama da bindigu 30 da babura 20, sannan an kashe mahara kusan 18 ciki har da Shanono.