Home Labarai Somaliya ta hana TikTok, Telegram da 1XBet

Somaliya ta hana TikTok, Telegram da 1XBet

0
Somaliya ta hana TikTok, Telegram da 1XBet

Somaliya ta haramta yin TikTok, da manhajar aika saƙo ta Telegram da kuma amfani da kamfanin caca na yanar gizo mai suna 1XBet, da nufin daƙile yaɗuwar batsa da farfaganda, in ji ministan sadarwa na ƙasar.

“Ministan sadarwa ya umurci kamfanonin intanet da su dakatar da aikace-aikacen da aka ambata a baya, wadanda ‘yan ta’adda da kungiyoyin fasikanci ke amfani da su wajen yada munanan hotuna da labaran ƙarya ga jama’a,” in ji Ministan, Jama Hassan Khalif, a cikin wata sanarwa.

Mambobin kungiyar masu tayar da kayar baya ta al-Shabaab sukan yaɗa ayyukansu a TikTok da Telegram.

Matakin na zuwa ne kwanaki bayan shugaban kasar Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud ya ce farmakin soji kan kungiyar al-Shabaab na da nufin kawar da kungiyar dake da alaka da al Qaeda nan da watanni biyar masu zuwa.

Umurnin ya ba masu ba da sabis na intanet har zuwa ranar 24 ga Agusta su bi.

1XBet ya yadu a Somalia wajen aikata caca, musamman a kan wasannin ƙwallon ƙafa.

An yi barazanar haramtawa TikTok takunkumi a Amurka saboda alakarta da gwamnatin China.

Jihar Montana ta zama ta farko da ta haramta manhajar a watan Mayu.