Home Labarai SSANIP ga Tinubu: Ka fara biyan mafi ƙarancin albashi tun kafin ma’aikata su koma almajirai

SSANIP ga Tinubu: Ka fara biyan mafi ƙarancin albashi tun kafin ma’aikata su koma almajirai

0
SSANIP ga Tinubu: Ka fara biyan mafi ƙarancin albashi tun kafin ma’aikata su koma almajirai

Kungiyar manyan ma’aikata kwalejonin ilimi ta kasa (SSANIP) ta bayyana damuwarta kan jinkirin da aka samu wajen aiwatar da sabon mafi karancin albashin ma’aikata da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rattabawa hannu watanni biyu da su ka gabata.

Kungiyar ta yi gargadin cewa rashin daukar matakin da gwamnati ta yi na janyo wa ma’aikatan Najeriya tabarbarewar tattalin arziki da kuma talauci.

A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da Shugaban SSANIP, Kwamared Philip A. Ogunsipe, da Sakataren ƙungiyar, Kwamared Nura Shehu Gaya suka sanya wa hannu, a karshen taron Majalisar Zartaswa karo na 73 a Abuja, kungiyar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta aiwatar da shirin.

Ƙungiyar ta kuma jaddada cewa jinkirin na iya jefa ma’aikata cikin halin kunci, domin kuwa albashin da ake biyan su bai isa ya ke ba wajen biyan bukatun su na yau da kullum.

SSANIP ta kuma bukaci gwamnati da ta cika alkawarin da ta dauka na biyan bashin mafi ƙarancin albashin ma’aikata daga watan Maris na 2024 zuwa yanzu tare da tabbatar da cewa ma’aikata za su samu kudaden nasu da su ke bi har sai an aiwatar da sabon mafi karancin albashi.